Promote Your Music/Video
Join Our WhatsApp Group For UpdatesDJ A.B - 'Yar Boko' + Lyrics

Description: No description added.
Size: 4.13 MB
Duration: 00:04:25
Artist: DJ A.B
Views: 19556
Downloads: 9345
Added On: Dec 09, 2015 at 17:42
Lyrics:
INTRO

This is Thug Life Mixtape
My African Sisters Star
Ok Let's go
It's a killer by DJ A.B

CHORUS

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend ur money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

VERSE 1

Da 200 box natashi ina maneji
Naje wurin mai suya ya yanka min da kabeji
Na loda katin dari na kara Hommie na Bebeji
Ina ta faman magana shiru ashe ma bai ji
Network was poor as the rain was falling
Babu wurin chilling ko ina naje boring
Sai BB na ta ringing ashe yarinyar ke calling
Ina amsawa sai tace min darling
I need help pls A.B I need you
Come pick me up
And come with a car and don't forget to come with your ATM card
Maganar ta da dadi muryarta kaman Waka
Ta zuba min british english duk nabi na rude
Na nemo key dakin baba na nan take na bude
Na debi wasu kudi 'kar'kashin pillow na ware
Jikina sai rawa ya ke har na manta ma in kulle

CHORUS

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend ur money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

VERSE 2

Na manna mota a guje banda niyyar in tsaya
Gashi motar dana dauka ba mai ta kusa ta tsaya
Saina ga dan bunburutu by my right saina tsaya
Na bude mashi tanki saiya kara galan daya
Bayan na saka mai saina kama hanya
Ban ma san inda zani ba saina buga mata waya
Wai ashe ma tana gida sai nace gani nan zuwa
Harda cewa inyi sauri wai dan tana jin yunwa
Gidansu ba'a tuwo, Gidansu Ba'a koko
Bata san menene 'kuli ba balle ma ince rogo
Gashi ita bata girki abinci saidai a siyo
Diberan su yayi tafiya sai gani nan na iso
Daga gani na kawai ta daka wani tsalle
Ta rungumeni da karfi saura kadan ma in balle
Yarinyar nan fresh fuskarta babu bulle
Gashi tayi kwalliya malam jikintaa harda lalle

CHORUS

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend ur money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

VERSE 3

Na kaita shopping mall ta maida ni dan dako
Don ni kaina bana iya kirga kayan dana dauko
Yarinya 'Yar boko ta maidani kamar Tom
Yan mata 'Yan boko kuji tsoronsu kamar Bomb
Mun fito shiga mota wai ita zata tuka
I know you are tired baby koma can ka huta
Tai mun dadin baki ni kuma soko sai na bata
A tashin farko tai sama da yellow fever
Saboda haka police sukaa kaini station
Suka kira babana sukace yaronka na station
Ashe shima nema na yake sai gashi a station
The girl disappered from the messed up situation
Da babana ya shigo banji ta da dadi ba
Nasha duka nasha wahala ban cikin haiyacina
Wai sai nayi 2weeks sannan za'ai bailing dina
In kuma na fito wai za'a kaini rehouse

CHORUS

Wai bata cin tuwo kuma bata shan koko
Wai saidai coke ita bata shan zobo
Ita bata hawa machine wai sai dai motor
Ni na shiga uku na dauko 'Yar boko
In kaji ta kiraka she want spend your money
In Kaji tana ta karyar turanci she want spend ur money
To gani nan dai na faka, she want chop my money
Eh nina shiga uku na dauko 'Yar Boko

Comment Form is loading comments...

RELATED MUSIC


CATEGORIES

Videos Videos
Music Music
Movies Movies
Android Android Zone

LIKE US ON FACEBOOK
About Us | Disclaimer | Privacy Policy | Nigerian Movies

FacebookTwitterInstagram